Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ‘yarsa, da wasu mutane biyu a kan kuɗi naira miliyan 100.
Ku tuna cewa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta yi tuhume-tuhume shida kan tsohon ministan, ‘yarsa, da wasu mutane biyu.
EFCC ta zargi Sirika da baiwa wasu kamfanoni damar da bai kamata ba tsakanin Afrilu 2022 zuwa Maris 2023 a Abuja.
Hukumar ta kuma zargi ministan da laifin amfani da ofishinsa ta hanyar da bata dace ba saboda ya ba da kwangilar naira biliyan 1.3 na Sabon Kamfanin Jirgin Saman Nijeriya ga kamfanin Tianero Nigeria Limited.