Back

Kotu ta hana Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa ƙara kuɗin wutar lantarki

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da umarnin wucin gadi na dakatar da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Kano (KEDCO) daga aiwatar da sabon ƙarin kuɗin wutar lantarki ga masu amfani da wutar na Band A.

Kwanan nan NERC ta umarci kamfanonin rarraba wutar lantarki da su ƙara wa masu amfani da wutar lantarki na Band A kuɗin wutar lantarki don samar da tsayayyen wutar lantarki ga waɗanda za su iya biyan kuɗin.

Sai dai da yawa daga cikin ‘yan Nijeriya sun soki NERC don yin ƙaura da akasarin masu amfani da wutar zuwa Band A yayin da ake fama da rashin wutar duk da hakan.

Duk da haka, Mai Shari’a A.M. Liman na Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, a ranar Alhamis, ya bayar da umarnin wucin gadi a matsayin martani ga wani kuɗurin da A.B Mahmoud, SAN, mai wakiltar Super Sack Company Limited, BBY Sacks Limited, Mama Sannu Industries Limited, Dala Foods Nigeria Limited, Tofa Textile Limited, da kuma Manufacturers Association of Nigeria Limited (MAN), a matsayin masu neman hanin, ya gabatar.

Hukuncin ya haramtawa NERC da KEDCO aiwatar da ƙarin kuɗin wutar lantarkin da aka tsara zai fara aiki a wannan watan, har sai an saurari ƙarar da kuma yanke hukunci kan ƙudirin.

Bugu da ƙari, odar ta haramta wa waɗanda ake tuhuma tsoratarwa ko barazanar yanke wutar lantarkin masu neman saboda rashin amincewarsu da sabon ƙarin kuɗin wutar lantarkin.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?