Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta Babbar Kotun Kano da ke zamanta a kan titin Miller, ta hana ‘yan sanda da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS) da sojojin Nijeriya korar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da aka mayar.
Sarkin ya shigar da ƙarar ne tare da masu naɗa sarakunan Kano huɗu: Madakin Kano Yusuf Nabahani; Makaman Kano Ibrahim Sarki Abdullahi; Sarkin Bai Mansur Adnan da Sarkin Dawaki Maituta Bello Tuta.
Da take bayar da wannan umarni, Mai Shari’a Amina ta kuma hana jami’an tsaro kamawa ko muzgunawa Sarkin da masu naɗa sarakunan.
Alƙalin ta ce, “An ba da umarni na wucin gadi na hana waɗanda ake ƙara ko dai ta kansu, wakilansu, masu zaman kansu, da wakilai, da waɗanda suka sanya ci gaba da cin zarafi, tsoratarwa, gayyata, kamawa da kuma mamaye wani gida ko na hukuma na masu shigar ƙara ( Gidan Rumfa), bayinsa ko wani daga cikin masu naɗa sarakunan Kano yin ayyukan da za su iya yin katsalanda ga haƙƙin masu ƙara a gabaɗaya dangane da wannan ƙarar har sai an saurari ƙarar da kuma yanke hukunci.
“An ba da umarni na wucin gadi wanda ya hana waɗanda ake ƙarar yunƙurin ƙwace wani daga cikin tagwayen mashin mulki, hularT Sarauta ta Dabo, takalman fuka-fukan jimina, wuƙa da takobin Sarkin Kano da kuma alamomin hukuma har sai an saurari ƙarar da kuma yanke hukunci.
“Wannan umarni na wucin gadi ya hana waɗanda ake ƙaran daga ɗaukar wasu matakai dangane da lamarin har sai an saurari ƙarar da kuma yanke hukunci.
“An ƙara ba da umarnin cewa waɗanda ake ƙara kada su yi katsalanda a cikin ayyukan mai ƙara na 1 a matsayin Sarkin Kano har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraren ƙarar mai kwanan wata 28 ga Mayu, 2024.
An ɗage sauraren ƙarar zuwa ranar 13 ga Yuni, 2024.
Mai shari’a Amina ta bayar da umarnin korar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga ƙaramar fadar Nassarawa ranar Litinin.