
Tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele
Mai Shari’a Rahman Oshodi na Kotun Laifuffuka na Musamman a Jihar Legas da ke Ikeja, a ranar Litinin, ya mayar da tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, hannun Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC).
Zai ci gaba da zama a gidan yari har zuwa ranar Alhamis, lokacin da alƙali zai yanke hukuncin neman belinsa.
Mai Shari’a Oshodi ya yanke wannan hukuncin ne bayan Emefiele da wanda ake ƙaransu tare, Herry Omoile, sun ƙi amsa laifin wasu sabbin tuhume-tuhume 26 da EFCC ta shigar da suka shafi amfani da ofis ta hanyar da bata dace ba.
Sai dai alƙalin kotun, ya bayar da umarnin tsare Omoile a gidan yari na Hukumar Gyaran Hali ta Nijeriya (NCoS).
Lauyan wanda ake ƙara, Abdulakeem Ladi-Lawal, ya buƙaci kotun da ta sanya irin sharuɗɗan belin da Mai Shari’a Hamzat Muazu na Babbar Kotun Birnin Tarayya Abuja ya bayar a baya da kuma a sake shi ga lauyoyinsa har sai an cika sharuɗɗan belin.
Lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo (SAN), bai ƙalubalance neman belin ba, sai dai ya buƙaci alƙali da ya sanya wasu sharuɗɗa da za su tilasta wa waɗanda ake tuhuma su zo kotu domin shari’ar su.
An tuhumi waɗanda ake tuhumar da karɓar cin hanci, karɓar kyaututtuka ta hanyar wakilai, da almundahana, da kuma kuɗaɗen damfarar dukiya.
An kuma zarge shi da bayar da cin hanci da rashawa ga abokan hulɗar sa saɓanin Dokar Cin Hanci da Rashawa, 2000 a tuhumar da mai gabatar da ƙara na EFCC, Rotimi Oyedepo (SAN) ya shigar a ranar 3 ga Afrilu, 2024.