
Abdullahi Umar Ganduje
Wata Babbar Kotu a Kano ta sanya ranar 17 ga Afrilu, 2024, a matsayin ranar da za ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje, da matarsa, da wasu mutane shida.
Waɗanda ake tuhumar za a gurfanar da su a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume takwas da suka haɗa da zargin karɓar cin hancin dala, karkatar da kuɗaɗen da suka haɗa da cin hancin dala 413,000 da naira biliyan 1.38 da dai sauransu.
A cikin takardar sammacin, sauran waɗanda ake ƙara sun haɗa da Abdullahi Umar Ganduje, Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd da Lesage General Enterprises.
Gwamnatin Jihar Kano a ƙarar da ta shigar a kan waɗanda ake ƙara su 8 ta ce ta haɗa shaidu 15 domin su bayyana a gaban Kotu.
An tsayar da ranar 17 ga Afrilu 2024 a gaban Mai Shari’a Usman Na’aba na Babbar Kotun Jiha mai lamba huɗu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Mai Shari’a na Jihar, Haruna Isah Dederi, ya ce an shigar da ƙarar, kuma za a gurfanar da duk waɗanda abin ya shafa.
Babban Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar, Haruna Isah Dederi, ya tabbatar da cewa Ganduje, matarsa da wasu mutane shida za a gurfanar da su a ranar da aka bayyana.
Ya ce, “Gaskiya ne. Mun shigar da ƙarar kuma za a yi shari’a a ranar 17 ga Afrilu, 2024. Abin da ba zan iya tabbatarwa ba shi ne ko an ba shi ko ba a ba shi ba amma tabbas za a ba shi.
“Abin da shi (Ganduje) bai fahimta ba shi ne, ba za ka iya guje wa wannan muguwar ranar ba, tabbas za ta zo maka, kuma hakan ma zai zama hani ga dukkan mu da muke cikin gwamnati a yanzu.
“Ya na cewa ba za mu iya gurfanar da shi ba yayin da ya manta cewa laifin ma yana ƙarƙashin nau’in laifuffukan jihar ne. Ba maganar Tarayya gaba ɗaya ba ce, kuma mun ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Mai Shari’a Liman ya yanke.”