Back

Kotu ta umarci Gwamnatin Tarayya ta saukaka farashin kayan masarufi cikin kwanaki 7

A ranar Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta umurci gwamnatin tarayya da ta saukaka farashin kayayyakin masarufi da na man fetur cikin kwanaki bakwai.

Mai shari’a, Ambrose Lewis-Allagoa  ne yayi umarnin da gwamnatin ta gyara farashin masarufi, musamman na madara, gari, gishiri, sukari, kekuna, da kayan sarrafa su. Sauran kayan su ne irin su ashana, babura da kayan aikinsu, motoci, kayan aikinsu da kuma kayayyakin man fetur, wanda ya hada da gas, bakin mai da kananzur.

Alkalin ya bayar da umarnin ne a lokacin da yake yanke hukunci a wata kara mai lamba FHC/L/CS/869/2023 da mai ra’ayin kare hakkin dan Adam, Mista Femi Falana, ya shigar a kan hukumar kula da farashin kayayyaki, ya hada da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, wanda aka lissafa a matsayin wadanda ake tuhuma na daya da na biyu.

Falana ya garzaya kotu domin tantance ko bisa ga sashe na 4 na dokar kayyade farashin, wanda ake kara na farko yana gudanar da aikin shi na sanya farashi kan duk wani kaya da aka kayyade a jadawalin farko na dokar kayyade farashin. 

A zaman da aka yi a ranar Laraba, mai shigar da karar, Cif. Femi Falana ya sanar wa da kotun cewa an gabatar da karar ne bisa sashe na 4 (1) na dokar tsara farashi na dokokin Tarayyar Najeriya, 2004.

Ya kuma shaida wa kotun cewa wadanda ake karar, tun lokacin da aka shigar da karar a watan Mayu na shekarar da ta gabata sun ki bada amsa akan abubwan da ake tuhumar su.

Don haka Falana ya bukaci kotun da ta yi duk wasu sauyi da ake nema tun da babu wata bukata da wadanda ake karar suka gabatar.

Mai shari’a Lewis-Allagoa, bayan ya saurari jawabin lauyan, ya Yi nuni da cewa wadanda ake karar ba su shigar da wata kara ko koke wadda zata hana ci gaba da ita wannan shari’ar ba. 

Saboda haka Alkalin ya yanke hukuncin cewa kotun ta gamsu, Kuma ta aminta da dukkan abubuwan da ke kunshe a cikin takardar karar da Falana ya gabatarwa kotun kamar yadda mai karan ke bukata.

Falana, a cikin takardar shaidar goyon bayan bukatar da lauyan shi ya gabatar a zauren sa, Taiwo E. Olawanle, ya bayyana cewa, wanda ake kara na farko, itace hukumar kula da farashi, wadde da ikon ta kafa dokar kafa farashi, kuma tana da alhakin da ya rataya a wuyanta. don daidaita farashin kaya, hana boye kayayyaki, kare hakkin masu siyen kayayyaki kan farashi mai tsada, da sauransu.Wanda ake tuhuma na biyu kuma shi ne babban jami’in shari’a na Najeriya.

Lauyan, ya kuma bayyana cewa, wanda ya shigar da karar ya shafe sama da shekaru 30 yana taka rawa wajen kare hakkin bil’adama da kuma kare hakkin bil’adama a Afirka, kuma saboda ayyukansa na kare hakkin bil’adama, kungiyoyi da dama na cikin gida da na kasa da kasa sun karrama mai karar.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?