Back

Kotu ta umarci ‘yan sanda da su kori tsohon Sarki Aminu Ado daga ƙaramar fada

Mai Shari’a Aisha Adamu Aliyu ta wata Babbar Kotu a Jihar Kano ta umarci Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano da ya kori Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

A cikin takardun kotun, alƙalin ta bayar da umarnin “hana waɗanda ake ƙara na 1, 2, 3 na 4 da na 5 ko dai da kansu, ko bayi, ko masu zaman kansu, ko kuma duk wani mutum ko jami’in da ke aiki a ƙarkashinsu ko kuma yana aiki da su da bayyana su a matsayin Sarakunan Kano, Bichi, Gaya, Rano da Ƙaraye har zuwa lokacin da za a saurari ƙarar da kuma yanke hukunci a kan ƙarar da masu ƙara suka shigar.

“An ba wa Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano umarnin ya gaggauta karɓe fadar Sarkin Kano da ke State Road Kano sannan ya kori wanda ake ƙara na 1 daga fadar har zuwa lokacin da za a saurari ƙarar da kuma yanke hukunci a kan ƙarar mai kwanan wata 24 ga Mayu, 2024.

“Wannan Kotun Mai Alfarma ta amince da dakatar da waɗanda ake tuhuma na 1, 2, 3 na 4 da na 5 daga gabatar da kansu a matsayin sarakunan Kano, Bichi, Gaya, Rano da Ƙaraye don neman zaman lafiya a Kano har sai an saurari ƙarar da kuma yanke hukunci kan ƙarar.”

Waɗanda ake ƙarar sun haɗa da Sarakunan Ƙaraye, Gaya, Bichi, Rano, Kano da aka sauke, tare da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Daraktan DSS, NSCDC da Sojoji.

Waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da Babban Lauyan Jihar Kano, Kakakin Majalisar Dokoki da Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?