Mai Shari’a Muhammad Nasir Yunusa na Babbar Kotun Tarayya a ranar Litinin ya yanke wa wasu ‘yan canji 17 a Jihar Kano hukunci bisa samun su da laifin yin kasuwanci ba tare da lasisin da ya dace ba, wanda hakan ya saɓa wa sashe na 57(5) (b) na dokar Bankuna da Cibiyoyin Kuɗi na shekarar 2020.
An yanke wa kowane mai laifin hukuncin ɗaurin wata 6 ko kuma tarar naira 50,000.
Mutanen da aka yankewa hukuncin da suka haɗa da Ayuba Ibrahim, Idris Saidu, Idris Usman, Shuaibu Muhammad, Hamisu Ilyasu, da wasu mutane 12, sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi a lokacin da ake sauraron ƙarar.
A wani samame na haɗin gwiwa ne jami’an ‘yan sanda da jami’an Hukumar Farin Kaya (DSS) suka cafke ‘yan canjin 17 a kasuwar Wapa da ke ƙaramar hukumar Fagge a makon jiya.
Bayan kama su, jami’an tsaro sun ƙwace kuɗin CFA 68,000 da kuma rupee 30,000 daga hannun waɗanda ake zargin a matsayin shaida kan ayyukan da suka yi ba bisa doka ba.