Back

Kotu za ta saurari ƙara kan dakatar da Ganduje a ranar 28 ga Mayu

Abdullahi Ganduje

Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman na Babbar Kotun Tarayya dake Kano, ya sanya ranar 28 ga watan Mayu domin sauraren ƙarar da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya shigar.

Ganduje yana ƙalubalantar dakatar da shi daga jam’iyyar da wasu shugabannin unguwanni suka yi ƙarƙashin jagorancin wani Basiru Nuhu.

Shugabannin APC, shiyyar Ganduje, ƙarƙashin jagorancin wani Haladu Gwanjo ne suka fara dakatar da shi a ranar 15 ga watan Afrilu, wani ɓangaren kuma ya sake bayyana dakatar da Ganduje a ranar 20 ga Afrilu.

Ganduje na neman a bayyana cewa dakatar da shi daga jam’iyyar ba tare da ba shi damar kare kansa ba, hakan ya saɓa wa haƙƙinsa na adalci.

Yana kuma neman a bayyana cewa dakatarwar da ɓangaren suka yi ya saɓawa doka.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?