Back

Kotun Kano ta tabbatar da dakatar da Ganduje

Abdullahi Ganduje

Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta tabbatar da dakatar da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje.

Kotun, yayin da ta ba da umarnin, ta kuma hana Ganduje ci gaba da bayyana kansa a matsayin ɗan jam’iyyar.

Mai Shari’a Usman Malam Na’abba ne ya bayar da umarnin a ranar Talata.

Umurnin ya biyo bayan ƙarar da Haladu Gwanjo da Laminu Sani suka shigar ta hannun lauyansu Ibrahim Sa’ad.

Masu shigar da ƙarar, waɗanda suka bayyana cewa su ne shugabannin zartarwa na shiyyar jam’iyyar APC ta Ganduje, sun ce sun kawo ƙarar ne a madadin shugabannin zartaswa na yankin.

Gwanjo, wanda ya bayyana a matsayin mai ba jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a, shi ne ya sanar da dakatar da Ganduje kwanaki biyu da suka gabata.

Bayan haka, kotun ta ba da umarnin cewa, daga yanzu, Ganduje ya daina jagorantar duk wasu al’amuran Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC) na APC.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?