Kwamitin Majalisar Wakilai kan Yaƙi da Zazzaɓin Cizon Sauro da Cutar Ƙanjamau da Tarin Fuka ya baiwa Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Mohammed Ali Pate, da babbar sakatariya, Daju Kachollom, wa’adin sa’o’i 72 su gurfana a gabansa bisa zargin karkatar da dala miliyan 300 na yaƙi da zazzaɓin cizon sauro tun 2021.
Kwamitin ya yanke shawarar cewa a kama babbar sakatariyar idan ta kasa mutunta sammacin, bayan ta kasa bayyana a gabansa bayan gayyata sau uku a jere.
Ana kuma sa ran za su amsa tambayoyi kan zarge zargen hana ’yan asalin ƙasar da ke ƙera gidajen kashe ƙwari samun kwangilar samar da ragar maganin ƙwari da kayayyakin da suka dangance su.
Shugaban kwamitin, Honarabul Amobi Godwin Ogah, wanda ya karanta ƙudurin kwamitin a taron da suka koma, ya nuna rashin jin daɗin mambobinsa kan rashin halartar babbar sakatariyar.
Ogah ya ce: “A yanzu zazzaɓin cizon sauro ya zama annoba a Nijeriya. Gwamnati a kodayaushe tana son taimakon jama’a, amma mafi yawan lokuta ma’aikatan gwamnati ne matsalarmu. An samar da wannan kuɗin tun 2021. Muna gayyatar babbar sakatariyar. Wannan shi ne karo na uku da muke gayyatar ta ta zo ta yi mana bayanin abin da ya faru.
“Shin sun yi amfani da kuɗin ne? Idan ba su yi amfani da kuɗin ba, ina kuɗin? Al’amari ne mai sauƙin bayani. Amma sun yi ta gudu suna kiran mutane iri-iri don su yi magana da mu. Amma muna nan don kare ’yan Nijeriya. An zaɓe mu ne mu wakilci jama’armu. ‘Yan Nijeriya ba za su ci gaba da mutuwa sakamakon kamuwa da cutar zazzaɓin cizon sauro ba, duk da cewa gwamnati ta yi duk wani ƙoƙari na ganin an kawar da ita nan da shekarar 2030.
“Majalisar Dokokin Ƙasar ba za ta ƙara amincewa da halin da ma’aikatan gwamnati ke yi na yaudarar majalisar ba. Ya isa haka. Jama’armu ne suka zaɓe mu mu wakilce su. An zaɓe mu ne don mu yi magana a madadin su kuma mu kare su. Kuma muna magana ne game da cutar da ta zama annoba. Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen neman ‘yancinmu da tsarin mulki ya ba mu na tilasta wa a kama babbar sakatariyar idan ta kasa mutunta sammacin,” inji shi.