Back

Ku kwantar da hankalinku, za a yi adalci, inji Aminu Ado Bayero ga mutanen Kano

Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano na 15, ya ce babu wanda ya fi ƙarfin doka, za a yi adalci, yana mai kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu.

Da yake jawabi a ƙaramar fadar da ya ke tun dawowar sa jihar bayan an sauke shi daga karagar mulki, ya ce za a yi adalci.

Sarkin ya sha alwashin amincewa da duk abin da doka ta ce, inda ya ƙara da cewa Kano jiha ce mai muhimmanci a Nijeriya.

Da yake magana, ya ce, “Ina kira ga jama’a da su ci gaba da bin doka da oda yayin da suke jiran sakamakon shari’a a wannan rikici.

“Muna kira ga hukuma da ta yi adalci a wannan lamarin. Kano jiha ce mai matuƙar tasiri a Nijeriya. Duk abin da ya shafi Kano ya shafi Nijeriya. Allah ya sa a zauna lafiya a Kano. Muna addu’ar Allah ya albarkaci Kano da shugabanni masu gaskiya da adalci.

“Adalci ita ce hanyar da za a bi a kowane lamari. Za a yi adalci. Babu wanda ya fi ƙarfin doka. Za mu yarda da duk abin da doka ta ce. Ina godiya ga duk mutanen da suka nuna damuwa.

“Za mu ci gaba da addu’ar zaman lafiya a Jihar Kano. Allah Ta’ala Ya tsare mu”.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?