Back

Ku nemi watan Ramadan 2024 Lahadi, inji Sultan ga musulmai

Alhaji Sa’ad Abubakar, Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA).

Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya, NSCIA, a ƙarƙashin jagorancin Shugabanta kuma Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta buƙaci al’ummar musulmi a faɗin ƙasar nan da su nemi ganin watan Ramadan na shekarar 2024 (shekara ta 1445 bayan hijira) daga Lahadi.

Farfesa Salisu Shehu, Mataimakin Sakatare Janar na NSCIA ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a cikin wata sanarwa.

A cewarsa, Sarkin Musulmi Abubakar yana taya ɗaukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar azumin watan Ramadan na shekara ta 1445 bayan hijira.

Majalisar tana addu’ar Allah ya raya kowane musulmi ya samu damar aikin ibadan, Ya kuma ƙara amfanin dake cikinsa.

Ya kuma kawo wata ayar Alkur’ani mai girma cewa watan Ramadan shi ne wanda aka saukar da Alkur’ani a cikin sa, wanda shiriya ne ga mutane kuma hujja bayyananne kan shiriya da bambanci tsakanin gaskiya da ƙarya.

“To, wanda ya ga jinjirin watan Ramadan daga cikinku, to, ya azumci wannan wata” (Baqarah: 185).

“Sakamakon shawarar Kwamitin Ganin Wata na Ƙasa (NMSC), Shugaban Ƙasa ya umurci al’ummar Musulmin Nijeriya da su nemi jinjirin watan Ramadan bayan faɗuwar rana a ranar Lahadi 10 ga Maris, 2024 wanda ya yi daidai da 29 ga watan Sha’aban, 1445 AH.

“Idan musulmi suka ga jinjirin watan da maraice, to mai martaba (Sultan) zai ayyana Litinin 11 ga Maris 2024 a matsayin ranar farko ta Ramadan 1445AH. Idan kuma ba a ga jinjirin watan ba a wannan ranar, to, Talata 12 ga Maris, 2024, za ta zama farkon watan Ramadan, 1445AH,” inji Shehu.

Ya kuma ce, a halin da ake ciki na wahalar tattalin arziƙi, majalisar ta yi kira ga al’ummar Musulmin ƙasar nan da su ƙara kai agaji ga marasa galihu da ke yankunansu kafin watan Ramadan da kuma bayan watan Ramadan.

Majalisar ta kuma shawarci ‘yan kasuwa da kada su riƙa tara kayan abinci, ko kuma su ƙara farashin kayayyakin masarufi a lokacin azumi.

Ya kuma buƙaci al’ummar musulmi da su yi amfani da wannan watan na Ramadan su yi addu’ar Allah Ya tallafawa Falasdinawa, Ya kuma ‘yantar da su daga azzalumai.

“Majalisar ta umarci al’ummar Musulmi a duk faɗin ƙasar nan da su sanya ido kan ganin jinjirin watan Ramadan a daren ranar Lahadi 10 ga watan Maris 2024 tare da jiran sanarwar da Mai Martaba Shugaban NSCIA zai bayar a hukumance kan fara azumin watan Ramadan ta shekerar 1445 bayan hijira.

“Muna yiwa ɗaukacin musulman Nijeriya da takwarorinsu na duniya barka da azumin watan Ramadan,” inji Shehu.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?