Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin ya buƙaci gwamnonin jihohi su samar da filayen kiwo ga makiyaya.
Tinubu ya ce samar da filayen kiwo ga makiyaya zai kawo ƙarshen rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya da asarar rayuka da amfanin gona.
Ya kuma buƙaci gwamnonin da su biya ma’aikata albashi domin rage yunwa da ƙuncin rayuwa.
Shugaban ya yi wannan jawabi ne a wajen ƙaddamar da kayan aikin noma na inji da kuma wani gyara na tashar filin jirgin saman Bola Ahmed Tinubu da ke Minna, jihar Neja.
Ya ce, “Dole ne ku kula da jama’armu, kuma ku sake farfaɗo da noma da shirin kiwo.
Ban ga dalilin da ya sa Nijeriya ba za ta iya shayar da dukkan ɗaliban da ke makarantunmu da lita ɗaya na madara a kowace rana ba idan an yi amfani da tsarin kiwo da kyau.
“Ya kamata gwamnoni su samar da filayen, ni kuma a matsayina na Shugaban Ƙasa, na ƙuduri aniyar ba ku cikakken shirin da zai magance wannan matsala wajen kawar da yunwa daga doron ƙasa.”
Shugaba Tinubu ya ce Gwamnatin Tarayya za ta haɗa kai da jihohi domin kawo ƙarshen yunwa da wahala.
“Mun ga matakin jajircewa a nan, tun daga matakin jiha. Mun ga shugabanci. Nasarar kowane shugaba zai dogara ne akan ikonsa na yin abin da ya kamata ya yi a lokacin da ya kamata a yi,” inji shi.
Tun da farko, gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ce har yanzu aikin noma na ɗaya daga cikin muhimman matakan da gwamnatinsa ta ɗauka na magance ƙalubalen da ke tattare da muhimman sassan tattalin arziƙi da samar da wadata ga al’ummar jihar da ma ƙasa baki ɗaya.