Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa ta gargaɗi jama’a, musamman waɗanda ke da ‘yan uwa a ƙasashen waje, game da wani sabon shiri na damfara da wasu masu fakewa a matsayin jami’an NDLEA suke shiryawa.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya rabawa manema labarai a yanar gizon hukumar a ranar Asabar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa tana son sanar da jama’a musamman waɗanda ke da ‘yan uwa a ƙasashen ƙetare kan wani sabon shiri na ‘yan damfara da ke kwaikwayar jami’an NDLEA tare da kira ga ‘yan ƙasa da ba su ji ba, su sanar da su yadda aka kama ‘yan uwansu a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed (MMIA) dake Ikeja Lagos ko kuma wani filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa a Nijeriya da miyagun ƙwayoyi idan sun isa ƙasar.
“Bayan sun jefa ’yan uwan cikin firgici, sai ’yan damfara suka nemi miliyoyin naira domin a samu sauƙin sakin waɗannan mutane daga hannun Hukumar NDLEA. Mun daƙile da dama irin wannan yunƙurin a baya lokacin da iyalin suka kira hukumar don taimako ko ƙarin haske.
“A halin yanzu, akwai irin wannan lamarin da hukumar ta bincika. A wannan lamarin, ana ta yaɗa hoton wani ɗan Nijeriya da ke zaune a Amurka da wani faifan bidiyo na wani jami’in hukumar NDLEA da ke tattaunawa da wata ‘yar uwarsa ta biyan naira miliyan 5 don sako ɗan Nijeriyan da ke zaune a Amurka da ake zargin an kama shi a filin jirgin saman Legas ranar Juma’a 22 ga Maris da isowarsa da ‘haramtattun kayayyaki’.
“Kamar dai a lokutan baya, binciken mu ma ya nuna cewa abin da ya faruwa a yanzu aikin ‘yan damfara ne. Babu wani jami’in NDLEA da ke da hannu a cikin hirar faifan kuma wanda hotonsa ke maƙale da faifan da ake yaɗawa ba ya hannun mu a MMIA ko kuma wata rundunar mu a jiya ko a wata rana.
“An shawarci iyalin da ke da hannu a cikin wannan lamarin da kada su ba ‘yan damfara kuɗin su. An kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da ke da ‘yan uwa a ƙasashen waje da kada su bayyana tsare-tsaren tafiye-tafiye na ‘yan uwansu da kansu don gujewa masu aikata laifuka na makirci.
“Ga waɗanda suke da irin wannan matsalar, ku nemi taimako ko ƙarin haske ta kowane layin tuntuɓar mu.”