Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, a ranar Laraba, ta samu wani Fabian John Itafor da laifin tallar kuɗin Nijeriya tare da yanke masa hukunci.
Mai shari’a Kehinde Olayiwola Ogundare ne ya yanke wa Itafor hukuncin hidimar al’umma na tsawon watanni uku bayan ya amsa tuhumar laifin da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta yi masa.
Mai laifin, a cewar mai gabatar da ƙara, Abubakar S. Wara, an kama shi ne a ranar 24 ga watan Fabrairu, 2024, a Leisure Event Center, Titin Wale Olateju, Victoria Island, inda yake tallar sababbin kuɗi na naira.
Ya shaida wa kotun cewa a lokacin da aka kama mai laifin, an samu kuɗi naira 347,000.00, dala 1, da fam 50 a hannunsa.
Ya kuma shaida wa kotun cewa, aikin da ake tuhumar ya aikata ba bisa ƙa’ida ba, ya ci karo da Sashe na 21 (4) na Dokar Babban Bankin Nijeriya na shekarar 2007, kuma laifi ne da za’a iya hukunci akai a ƙarƙashin wannan doka.
Laifin da ake tuhumar mai laifin ya ce: “Kai Fabian John Itafor, a ranar 24 ga Fabrairu, 2024 a Leisure Event Center, Titin Wale Olateju, Victoria Island, a Legas da ke ƙarƙashin ikon wannan Kotu mai girma, ka yi tallar naira 347,000.00 (naira ɗari uku da arba’in da bakwai) da Babban Bankin Nijeriya ya bayar kuma ka aikata laifin da ya saɓawa Sashe na 21(4) na Dokar Babban Bankin Nijeriya na shekarar 2007.”
Mai laifin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi lokacin da aka karanta masa. Bayan ya amsa laifinsa kamar yadda ake tuhumar, mai gabatar da ƙara ya buƙaci kotun da yanke masa hukunci daidai da sashen na Doka, da aka tuhume shi da aikata laifin.
Sai dai mai laifin ta bakin lauyansa, wanda ya yi iƙirarin cewa wannan ne karo na farko da ya aikata laifin, ya roƙi a yi masa sassauci kuma ya sha alwashin ba zai sake irin wannan aikin ba.
Lauyan nasa ya kuma roƙi kotun da ta yi la’akari da zaɓin tara da za ta yi a maimakon hukuncin ɗaurin rai da rai.
Mai shari’a Ogundare, bayan da mai gabatar da ƙara ya tabbatar da cewa wanda aka yankewa laifin shine karo na farko da ya aikata laifin, kuma ba tare da wani tarihin aikata laifin da aka yanke masa ba, ya yanke masa hukuncin ɗaurin watanni uku, amma ya umarce shi da ya biya naira 50,000,00 a madadin hukuncin.
Alƙalin ya kuma ƙwace na’urar POS na mai laifin da kuɗi naira 347,000,00; dala 1, da fam 50, da aka samu tare da shi a lokacin kama shi.