Back

Kungiyar dillalan man fetur ta Enugu ta yi barazanar yajin aiki kan tsawwala haraji 

Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta, (IPMAN) ta Depot na garin Enugu, ta yi gargadin cewa za ta tilasta rufe sayar da man fetur a jihar Anambra nan da makonni biyu masu zuwa saboda hare-haren da ake kaiwa ‘yan kungiyar.

Kungiyar ta zargi gwamnatin Gwamna Chukwuma Soludo da sakawa ‘yan ƙungiyar ta haraji fiye da kima, tare da dakile harkokin kasuwancin su da kuma kama su.

Shugaban kungiyar ta IPMAN, Chinedu Anyaso, wanda ya yi wannan gargadin a ranar Juma’ar da ta gabata, jim kadan bayan da aka sake zaban shi domin gudanar da harkokin ‘ya’yan kungiyar, a karo na biyu na tsawon shekaru uku, ya yi alkawarin cewa zai ci gaba da yin aiki tukuru domin magance matsalolin da mambobin kungiyar ke fuskanta.

A cewar shi, duk kokarin da ƙungiyar ta yi na jawo hankalin gwamnatin jihar kan lamarin ya ci tura kuma ba a samu wani sakamako mai amfani ba.

Ya yi nuni da yadda aks kai wasu ‘yan ƙungiyar ta IPMAN da ke sana’o’in su a jihar Anambran kotu aka daure su, ko aka ci tarar su saboda kin bin doka da ta wuce ka’ida da kuma kin biyan harajin da aka tsawwala musu.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?