Kungiyar Kare Hakkokin Zamantakewa da Tattalin Arziƙi SERAP ta maka Akpabio da Abbas ƙara kan rashin yin ƙarin haske bisa kasafin N344.85bn na Majalisar Dattawa
Ƙungiyar Kare Haƙƙokin Zamantakewa da Tattalin Arziƙi (SERAP) ta shigar da ƙarar Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudfeen Abbas, a kan rashin bayyanawa, fayyacewa da kuma yin bayani game da kasafin kuɗin Majalisar Tarayya na fiye da Biliyan dari uku da arb’a’in da hudu (N344.85,) da kuma dalilan da suka shafi kasafin kuɗi da dama, kamar Naira biliyan shida da aka kasafta wa wuraren ajiye motoci guda biyu na majalisun.
Ana tuhumar Akpabio da Abbas ne, kuma a madadin ɗaukacin ‘yan majalisar dokokin.
A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/178/2024 da ta shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babban Kotun Tarayya da ke Abuja, SERAP tana neman kotu tayi umarnin da tilasta Akpabio da Abbas su bayyana, su fayyace kuma su yi bayani game da kasafin kuɗin majalisar dokokin ta Ƙasa a cikin fokar Kasafin Kuɗi na wannan shekarar.
SERAP na neman: “umarnin mandamus da ya umurci da tilasta Mista Akpabio da Mista Abbas su bayyana, su fayyace kuma su yi bayani game da Naira biliyan 8.5 da aka ware wa ‘Alhakin Majalisar Dokokin Ƙasa’ a cikin dokar Kasafin ta na wannan shekarar.”
Har ila yau, tana neman: “umarni da tilasta Mista Akpabio da Mista Abbas su bayyana, su fayyace tare da bayani game da yadda aka kashe Naira biliyan uku domin’ Filin Ajiye Motoci na Majalisar Dattawa’ da kuma Naira biliyan uku na filin Ajiye motoci na Majalisar Wakilai a cikin dokar Kasafin na wannan shekarar.”
A cewar SERAP, “Tsarin kashe Naira biliyan 344.85 na kasafin kuɗin Majalisar Dokoki na ƙasa zai yi mummunan tasiri ga muhimman muradun ‘yan ƙasa da kuma amfanin jama’a.”
Ƙarar da lauyoyin ta, Kolawole Oluwadare da Andrew Nwankwo suka shigar a madadin SERAP, sun buƙaci kotun “domin amfanin jama’a da kuma shari’a ta yi wannan umurnin, domin ‘Yan Najeriya suna da ‘yancin samun damar bayanai da tsarin mulki da Kamar yadda duniya ta amince da su.”
SERAP ta ce, Amfanin jama’a na samun bayanan da ake nema ya zarce duk wani amfani. Sa ido kan yadda jama’a ke samun irin waɗannan bayanai zai zama muhimmin bincike kan ayyukan ‘yan majalisar da kuma taimakawa wajen hana cin zarafin jama’a.
“Bayyanawa, fayyacewa da kuma yin bayani kan yadda aka kashe kasafin kuɗin Majalisar Dokokin Ƙasar zai inganta amincewar jama’a, da baiwa ‘yan Najeriya damar bin diddigin yadda ake kashe kuɗaɗen, da kuma tantance wa ko abubuwan da ke cikin kasafin kuɗin sun dace, da kuma buƙatar bayanai daga ‘yan Majalisar Dokoki a lokuta irin wannan.”
“Bayyanawa, fayyacewa da kuma yin bayani kan yadda ake son kashe Naira biliyan 344.85 na kasafin kuɗin Majalisar Dokokin ƙasar zai tabbatar da cewa ‘yan majalisar sun amsa wa jama’a domin gudanar da ayyukansu.”
Sai dai ba a ƙayyade ranar da za a saurari ƙarar ba.