Kungiyar Kwadago ta mayar da martani kan zargin amincewar da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi na kashe Naira miliyan dari biyar domin kaddamar da kwamitin mutane talatin da bakwai kan sabon mafi karancin albashi na kasa.
Idan za a iya tunawa, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya kaddamar da kwamitin mutane talatin da bakwai kan mafi karancin albashi na kasa a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa, Abuja, a ranar talatin ga watan daya na wannan shekarar.
Sai dai a wata wasika da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya aike wa shugaban kasa, ya nuna bukatar farko da aka mika wa Tinubu na kasafin kudi ne na Naira biliyan data da naira miliyan dari takwas, wanda ya ki amincewa.
Rahoton ya yi zargin cewa sakataren gwamnatin ƙasar, George Akume ya fara gabatar da wani kasafin kudi na Naira biliyan daya, amma Tinubu ya dage kan cewa kwamitin zai fara da Naira miliyan dari biyar.
Da yake mayar da martani game da wannan ci gaban, shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta Najeriya (NULGE), Akeem Ambali, ya bayyana damuwar shi kan Naira miliyan dari biyar da shugaban kasa ya amince wa kwamitin.
Ambali ya ce ba a taba yi wa kungiyoyin ƙodago bayanin kasafin kuɗin da aka aka amince a a kashewa kwamitin ba, inda ya kara da cewa shugabannin kungiyoyin kwadagon za su bayyana hakikanin al’amarin yayin taron kwamitin a ranar Litinin.
Ya ce, “Akan maganar rabon kudi ga kwamitin, abu ne da ba za a taba mantawa da shi ba, domin ba a taba sanar da mu ko ba mu kobo ba.”