Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce malamin addinin Islama na Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ba ya da hannu wajen dawo da ɗaliban Kuriga da aka sace, duk da cewa malamin ya yi tayin tattaunawa da ƴan bindigar domin a sako ɗaliban.
Gwamnan wanda ya bayyana hakan a cikin shirin Sunday Politics na gidan Talabijin na Channels ya ce sojoji tare da haɗin gwiwar hukumomi daga maƙwabtan jihar Zamfara inda masu garkuwan suka kai ɗaliban sun ceto ɗaukacin ɗalibai 137 da ‘yan bindiga suka sace a ranar 7 ga Maris, 2024 daga ƙaramar hukumar Chikun ta jihar.
Gwamnan ya bayyana maganganun da ake yi a wasu wurare na cewa an biya kuɗin fansa a matsayin shati faɗi, inda ya jaddada cewa Gumi ba ya da hannu wajen ceto yaran.
Sani ya ce, “Duk wannan shati faɗin da kuke ji a yau, tunanin wasu ne kawai. Zan iya gaya muku cewa, ba tare da wani tsoro na saɓani ba. Babu wani abu kamar Gumi a wannan aiki. Zan iya gaya muku. Ba zan yi watsi da ƙoƙarin Sojojin mu ba.”
Gwamnan ya kuma ce saɓanin rahotanni, ƴan makaranta 137 aka sace, ba 287 ba, a makarantar firamare ta LEA da makarantar sakandiren gwamnati da ke Kuriga, kimanin makonni huɗu da suka gabata.
Sani ya yi nadamar cewa malamin da aka yi garkuwa da shi tare da ɗaliban ya rasa ran sa saboda ya samu wasu matsaloli yayin da yake tsare. Ya yi ta’aziyya ga iyalan marigayin tare da jajantawa iyalan ƴan makarantar da aka sako.