Back

Kuriga: Batun an biya diyya bai da muhimmanci – Uba Sani

Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya bayyana cewa gaddama kan biyan kuɗin fansa domin kuɓutar da ɗaliban Kuriga da aka yi garkuwa da su ba shi da wani muhimmanci.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana a shirin Sunday Politics na Gidan Talabijin na Channels, inda ya ƙara da cewa abin da ke da muhimmanci shi ne gwamnati ta samu nasarar kuɓutar da dukkan su ba tare da an samu rauni ba.

Kimanin makwanni huɗu da suka gabata ne aka sace yaran a makarantar firamare ta LEA da kuma makarantar sakandare ta gwamnati da ke Kuriga amma hedikwatar tsaro a ranar Asabar ta ce an ceto su.

An yi ta jita-jita cewa gwamnati ta biya kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane domin a sako yaran, wanda Gwamna Sani ya yi watsi da shi.

Ya ce: “Abin da ya fi muhimmanci a yau shi ne yaranmu sun koma gida. Waɗancan maganganun basu da muhimmanci. Idan aka yi garkuwa da yaronka, za ka zauna kana magana kan yadda aka sako shi?

“A gare ni, abin da ya fi muhimmanci shi ne cewa waɗannan yaran sun dawo gida. Iyayen su suna matuƙar farin ciki kuma abin da ke da muhimmanci a gare su shi ne su sake haɗuwa da ’ya’yansu.

“Amma wasu mutanen da lamarin bai shafa ba su ne ke fitowa da wasu zarge-zargen da ba su dace ba game da ko an biya kuɗin fansa, ko an tunkari lamarin ta hanyar faɗa ko sasantawa. Abin da ke da muhimmanci a gare mu a Kaduna shi ne yaran sun koma gida.”

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ta ɗauki matakin da ya dace kan satar ‘yan makarantar Kuriga, inda ya ƙara da cewa: “Mun yi iya ƙokarinmu don kada mu jefa rayuwar yaran da ba su ji ba ba su gani ba cikin haɗari. Wasu mutane sun so su siyasantar da lamarin gaba ɗaya.”

Ya ce saɓanin rahotanni, an sace ɗalibai 137 ba 287 ba a ranar 7 ga Maris, 2024, daga Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun ta jihar.

“Ba na so in yi gaddama da kowa dangane da adadin. Abin da ya fi muhimmanci a gare ni shi ne dawowar yaran lafiya. A yau, na yi farin ciki da dawowarsu cikin ƙoshin lafiya, amma waɗannan adadi kawai na tunanin wasu mutane ne,”inji gwamnan.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?