Back

Kwamandan Boko Haram da ‘yan ta’adda 118 sun miƙa wuya a cikin wata 1

Rundunar Haɗin gwiwa ta Ƙasa da Ƙasa ta Operation Lake Sanity (MNJTF) ta sanar da miƙa wuyan kwamandan Boko Haram, Adamu Muhammad, da wasu mayaƙa 5, ga Sashe na 3 a Monguno, Jihar Bornon Nijeriya.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a ta bakin Babban Jami’in Yaɗa Labarai na Sojin N’djamena-Chad, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi.

Ya bayyana cewa adadin ‘yan ta’addan da suka miƙa wuya na baya-bayan nan tun bayan fara aikin Operation Lake Sanity ll a wata guda sun kai 119.

A cewarsa, ‘yan ta’addan sun tsere daga maɓoyar ƙungiyar ISWAP a Jubillaram, dake Kudancin Tafkin Chadi.

“Adamu, mai shekaru 22, yana da hannu cikin hare-haren ta’addanci da dama kuma ya zagaya garuruwan Kangarwa, Alagarno, Doro Naira, da Dogon Chikwu a ƙaramar hukumar Kukawa, Jihar Borno, Nijeriya.

“A lokacin da suka miƙa wuya, sun miƙa harsashi na musamman guda 11 na 7.62mm da harsashi guda ɗaya na yaƙi da jiragen sama.

“Sauran mayaƙan da suka miƙa wuya sun haɗa da; Isah Ali mai shekaru 18; Hassan Modu, mai shekaru 18; Nasir Idris, ɗan rakiyan Kwamandan Jubillaram Usman Rasha mai shekarau 23; Abba Aji mai shekaru 21 da haihuwa, Abubakar Isah, mai shekaru 20,” inji Laftanar Kanal Abdullahi.

Ya ƙara da cewa ana gudanar da bincike kan mayaƙan da suka miƙa wuya.

MNJTF ta yi kira ga sauran ‘yan ta’adda da su yi koyi da su, su ajiye makamansu, su rungumi zaman lafiya.

Ya ƙara da cewa, “Mun sake jaddada aniyarmu ta tabbatar da amintaccen muhalli a yankin Tafkin Chadi.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?