
Babban kwamandan hukumar Hisbah ta Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi murabus daga mukamin shi.
Daurawa ya mika takardar murabus ne cikin wani faifan bidiyo ma tsawon mintuna biyu da ya wallafa a shafin shi na Facebook a yau ranar Juma’a.
Murabus din nasa ya zo ne kasa da sa’o’i ishirin da hudu bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wa sabuwar hanyar gudanar da ayyukan da hukumar Hisbah ta bullo da shi na kama masu laifuka ba tare da kima da kiyaye yancin ‘yan Adam ba a lokutan yaki da munanan dabi’u a jihar.
Da yake jawabi ga Malamai a gidan gwamnati a ranar Alhamis, Gwamna Yusuf, ya yi kakkausar suka kan yadda ake mamaye wuraren tarurruka na jama’a da sunan kama karuwai, lamarin da ya ce bai dace ba.
Gwamna Yusuf ya kuma nuna takaicin yadda hukumar Hisbah ke kama wadanda ake zargi, yana mai cewa dole ne hukumar ta sake duba ayyukan da take yi a yanzu domin gyara kura-kuran da ke tsakanin al’umma.
Da yake mayar da martani kan kalaman Gwamna Yusuf, Daurawa ya bayyana cewa hukumar ta Hisbah a karkashin jagorancin shi ta fara gudanar da ayyuka da dama domin gyara rashin da’a da ake tafkawa a tsakanin al’umma, musamman masu tasiri a shafukan sada zumunta.
A cewar Sheikh Daurawa, Hisbah ta yi abin da ta yi imanin cewa daidai ne kuma a karkashin tsarin Musulunci.
Sai dai ya bayyana cewa ya yi murabus daga mukamin shi tare da yi wa gwamnan da gwamnatin shi fatan alheri