Back

Kwastam ta kama manyan motoci Sha biyar na kayan abinci a Sakkwato 

Hukumar Kwastam ta Najeriya, NCS, ta cafke manyan motoci goma Sha biyar dauke da kayan abinci a jihar Sokoto a wani mataki na hana fasa kwauri wanda ya assasa tsadar kayayyaki a kasar.

Kakakin hukumar rundunar ta jihar Sakkwato, Abubakar Tsafe, ne ya shaidawa manema labarai, a ranar Asabar, cewa an kama motocin ne a kan hanyar Gwadabawa zuwa Illela.

Kakakin ya ce, an yi kamen saboda yawan amfanin gonar da barayin ke dauke da su.

Ya ce a halin yanzu manyan motocin na hannun hukumar, kuma an fara bincike domin gano masu shi da inda za a kai kayan abincin.

Ya bayyana cewa rundunar hadin guiwa ta NCS ta Sokoto, jami’an sashin ayyuka na tarayya da kuma sashin leken asiri na hukumar ne suka gudanar da aikin.

Tsafe ya kara da cewa aikin ya zama dole tare da hauhawar farashin kayan abinci a kasar.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?