Back

Labarin juyin mulki karya ne, tsoratarwa ce – inji gwamnatin tarayya 

A jiya ne dai gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi watsi da rahoton da ke nuna fargabar juyin mulki a kasar, inda ta ce babu shakka karya ce kuma wani mummunan aiki ne na rashin gaskiya.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, wanda ya bayyana matsayin gwamnati, ya ce rahoton na daga cikin rugujewar hasashe na masu zagon kasa, wadanda mummunar manufar su ita ce ta dagula al’amura a cikin kasar nan da kuma yin zagon kasa ga gwamnati mai ci.

Idris ya ce gwamnati ba za ta dauke hankali ko razana ba wajen yin watsi da sauye-sauyen da ake yi da nufin farfado da tattalin arziki da samar da hanyar wadata ga ‘yan kasa.

Ya ce a yanzu ya tabbata cewa wasu mutane da ke cikin halin kaka-ni-kayi sun koma buga labaran bogi domin su gurbata tsakanin jama’a da gwamnati tare da haifar da fitina a kasar nan.

Idris ya ce gwamnati za ta yi amfani da ‘yancinta a cikin dokokin Tarayyar Najeriya don dakile ayyukan marasa kishin kasa ta yi ayyukan ci gaba da ba a taba gani ba domin farfado da arzikin kasa da magance tabarbarewar tsaro da kare dimokuradiyyar da kasar ta samo da kyar.

Ya bukaci jama’a da su hankalta, kuma su guji yada ko rarraba rahotanni da ba shi da tushe, wanda ake dasawa a kan wasu kafafen yada labarai da ba su dace ba don murkushe dimokradiyyar kasa.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?