Back

Laguda na APC ya lashe zaɓen Surulere, don maye gurbin Gbajabiamila

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na Mazaɓar Tarayya ta Surulere.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, Jami’in Zaɓen, Farfesa Simeon Adebayo, ya bayyana cewa ɗan takarar jam’iyyar APC ya samu ƙuri’u 11,203.

Laguda, Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC ne a Ƙaramar Hukumar Surulere shine ya maye gurbin Femi Gbajabiamila wanda aka naɗa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.

Gbajabiamila ya kasance Kakakin Majalisar Wakilai tsakanin 2019 zuwa 2023 kuma ya sake lashe zaɓensa a Majalisar a karo na shida a jere don wakiltar Mazaɓar Tarayya ta Surulere 1 a zaɓen Majalisar Tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu kafin a naɗa shi a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa tsakiyar 2023.

Gbajabiamila, ɗaya daga cikin manyan abokan Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas tsakanin watan Mayun 1999 zuwa Mayu 2007, ya yi murabus daga Majalisar Wakilai a watan Yunin da ya gabata, sannan Kakakin Majalisar Tajudeen Abbas ya bayyana babu kowa a kujerarsa wanda hakan ya sa a yi zaɓen fidda gwani a mazaɓar Surulere 1 domin cike gurbin.

Dubi Cikakken Sakamakon Zaɓen na Ranar Asabar:

ADC-40

APC- 11,203

APGA-6

AM-7

APP-4

LP-240

NNPP-8

PDP-278

SDP-2

YPP-9

ZLP-4

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?