Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya, Olukayode Egbetokun, a ranar Alhamis, ya ce an kai ƙarar ta’addanci 141, garkuwa da mutane 214 da kuma kisan kai 537 a cikin makonni takwas da suka gabata.
Egbetokun ya ƙara da cewa an kama mutane 3,685 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, yayin da aka ceto mutane 401 da aka yi garkuwa da su.
Egbetokun ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan jarida a Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Gidan Louis Edet, Abuja.
Ya ce, “Ina farin cikin bayar da rahoton wani gagarumin ci gaba, wanda aka samu ta hanyar aiwatar da dabaru daban-daban da nufin daƙile ƙaruwar miyagun laifuka a faɗin ƙasar nan bayan taron mu na ƙarshe da aka gudanar a ranar 8 ga Fabrairu, 2024.
“A cikin makonni takwas da suka gabata, mun samu ƙararraki 141 na ta’addanci/hare-haren ‘yan aware, da kisan kai 537, da fashi da makami 126, da sace-sacen mutane 214, da kuma laifuka 39 na mallakar bindigogi ba bisa ƙa’ida ba.
“Har ila yau, a tsawon lokacin da Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta kama mutane 3,685 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, an ceto mutane 401 da aka yi garkuwa da su, an ƙwato bindigogi iri-iri 216, alburusai 3,601 da motoci 82.
“A cikin watanni tara da suka gabata mun ba da kuɗi naira 7,263,391,051.73 ga iyalai 2,5143 na jami’an ‘yan sanda da suka rasu.”