
Kwamiti na musamman da ke kula da asusun lamuni na ilimi na Najeriya (NELFUND) ya gudanar da taron shi na farko a shirye-shiryen kaddamar da shirin a ranar Litinin ashirin da shida ga watan nan.
Taron dai ya gudana ne karkashin jagorancin gwamnan babban bankin kasar, Olayemi Cardoso, wanda kuma shine shugaban kwamitin na musamman.
Cardoso ya bukaci ‘yan kwamitin da su yi amfani da hikimomin su daban-daban don tabbatar da nasarar shirin, wanda yana daya daga cikin ayyukan sa hannun Shugaba Bola Tinubu.
Ya ce dole ne a kara kaimi wajen hada kai da masu ruwa da tsaki domin samun nasarar shirin ba tare da wani cikas ba.
Cardoso ya yi alkawarin bayar da himma da goyon bayan shi domin samun nasarar shirin, ya kuma yaba da jajircewar da shugaban kasar ya yi na shirin da zai rage nauyin bayar da tallafin karatu ga daliban Najeriya.
Babban makasudin dokar shine don haɓaka damar samun ilimi mafi girma ga ɗaliban Najeriya. Shugaba Tinubu ya nemi da a tsawaita shirin domin baiwa ‘yan Najeriya da ke koyon sana’o’in hannu.
Yin wannan taron na farko na dukkan bangarorin shari’a da ke cikin shirin, ya share fage na tsarin matakin kaddamar da asusun na karshe