Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya tabbatar wa ƴan kasuwa da ke kasuwanci a Lekki Free Zone alƙawarin da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta ɗauka na samar da ababen more rayuwa domin bunƙasa sarrafa kayayyaki a yankin.
Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a wani taron tattaunawa da wasu ƴan kasuwa da ke yankin Lekki Free Zone a fadar shugaban ƙasa, Abuja.
News Agency of Nigeria (NAN) ya ruwaito cewa ƴan kasuwan sun samu jagorancin Manajan Darakta na kamfanin Tolaram, Mista Haresh Aswani.
Shettima wanda ya yi magana jim kaɗan bayan ya saurari wani bayani kan hanyoyin kawo sauyi ga hanyoyi a cikin yankin Lekki Economic Axis, ya ce za a ba da fifiko ga hanyoyin da ke ɓangaren Lekki.
Ya ce ƙudurin gwamnati ya ginu ne kan “manyan fa’idodin tattalin arziki da zamantakewa da jama’a da gwamnati ke samu.
“Za mu kuma bincika yiwuwar buɗe sabbin hanyoyin samun dama ga ‘yan Najeriya.”
Ya ce abubuwan da Shugaba Tinubu ya yi a matsayin jagoran masu fafutukar kafa sana’a wata hanya ce da za ta zaburar da ci gaban yankin wanda ke da ɗimbin fa’idar tattalin arziki ga gwamnati da jama’a.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma tabbatar wa duk ƴan kasuwa da ke aiki a yankin da sauran wurare a kasar cewa gwamnatin Tinubu “tana kan hanyar kafa tarihi.”
“Za mu shawo kan dukkan kaluɓalen tare da magance matsalolin da ke yaƙi da ci gaban kasuwanci a kasar.
“A wata hira da manema labarai na gidan gwamnati, Darakta a tashar Lekki Deep Sea, Misis Adesuwa Ladoja, ta gode wa mataimakin shugaban ƙasa bisa yadda ya saurare su da kuma sauraron buƙatunsu. Ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ba da fifiko wajen samar da ababen more rayuwa a yankin Lekki Free Zone, la’akari da ɗimbin alfanun da take da su na tattalin arzikin ƙasa.
Har ila yau, babban jami’in gudanarwa na kamfanin Colegate Tolaram, Mista Girish Sharma, ya ce gyaran hanyoyi a cikin da kewayen yankin zai magance ƙalubalen da masu aiki a yankin ke fuskanta.
Ya nemi ƙarin tallafi ga kamfanoni a yankin irin su Tolaram Group, kamfanin da ke da jarin jari mai yawa a Najeriya a masana’antu, gine-gine da sauransu, ya ɗauke ƴan Najeriya sama da 20,000 aiki.
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Darakta-Janar na Nigerian Tourism Development Corporation (NTDC), Mista Folorunsho Coker, da Darakta a Lekki Free Zone, Mista Dinesh Rathi, da dai sauransu. (NAN)