Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta Ƙasa (FRSC) ta jihar Kaduna ta ce za ta fara sintiri na musamman na tsawon sa’o’i 24 a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja daga ranar Asabar don magance matsalar lodi fiye da ƙima, musamman na manyan motoci.
Kwamandan Sashin, Mista Kabir Nadabo, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya, NAN, ranar Juma’a a Kaduna cewa zasu gudanar da sintirin ne domin rage haɗurra da mace-mace a kan babbar hanyar.
Nadabo ya ce za a gudanar da sintirin na musamman ne tare da jami’an ‘yan sanda da na farin kaya da ƙungiyoyin sufuri da kuma Hukumar Kiyaye Hadurra ta jihar Kaduna (KASTLEA).
Ya ce za a sa duk motar da aka kama ta sauke fasinjoji da dabbobi da kayayyakin da ta ɗauka fiye da ƙima kafin a bar su su ci gaba da tafiya.
Nadabo ya ce za su samar da dukkan hanyoyin da suka dace domin rage yawan haɗurran da ke faruwa a kan tituna domin ceto rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.
“Bari in bayyana cewa rundunar tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro za su tabbatar da an cimma manufofin aikin.”
Ya ƙara da cewa, “Kwamandan Rundunar, Mista Dauda Biu tare da sauran kwamandojin ayyuka a jihar za su fara gudanar da aikin domin nuna muhimmancin sa,” inji shi.
Kwamandan rundunar ya bayyana cewa, manufar ita ce a samu babbar haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki, da tabbatar da gudanar da sintiri mai inganci da gaggawar ayyukan ceto tare da daƙile cikas a kan lokaci.
Ya ce al’amura na baya-bayan nan sun sa an ɗauki tsauraran matakai na daƙile haɗarin masu ababen hawa da ke wuce gona da iri wajen lodin fasinjoji da kayayyaki da kuma dabbobi da galibinsu ke tafiya da daddare.
“Sakamakon haɗarurrukan da waɗannan masu aikata laifukan kan tituna suka yi ya haifar da asarar rayuka da dama da kuma asarar dukiyoyi,” inji kwamandan sashin.
Nadabo ya ƙara da cewa, “Bisa bayanan da aka samu kan haɗurran kan tituna, daga Oktoba 2023 zuwa 21 ga Maris, 2024, Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta yi rahoton haɗarurruka 12 da suka haɗa da sama da mutane 500, 114 sun mutu, 210 kuma sun samu raunuka daban-daban.”
Kwamandan ya bayyana cewa yawancin matafiya sun fito ne daga jihohin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas da suka haɗa da Sokoto, Katsina, Zamfara, Kano, Jigawa, Kebbi, Bauchi, Yobe, Borno da Gombe da dai sauransu.
“Masu ababen hawa suna bi ta jihar Kaduna ne domin zuwa inda suke, galibi yankunan Kudu maso Gabas, Kudu maso Yamma, da Kudu maso Kudu na ƙasar nan.
“Waɗannan masu ababen hawa galibi suna tafiya ne cikin dare tare da haɗurran da suka fi faruwa a jihar Kaduna akan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
“Muna kira ga masu ababen hawa, musamman direbobin manyan motoci, da su daina lodin motocin su da dabbobi da mutane fiye da ƙima. Yana da matuƙar haɗari.
“Zuwa ga samarin da ke tafiya yankin kudancin ƙasar nan don kasuwanci ko sana’a, ina so in sanar da ku cewa hawa irin waɗannan motocin masu sauƙi don tafiye-tafiye yana jefa rayuwarku cikin haɗari.”