Back

Ma’aikacin POS na Kano ya dawo da naira miliyan 9.9 da aka yi kuskuren tura wa zuwa asusun bankin sa

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta miƙa kuɗi kimanin naira miliyan 9.9 da aka tura wa wani ma’aikacin POS ga mai su a Kasuwar Hatsin Dawanau da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta jihar.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a Kano ranar Alhamis.

Ya ce wani ma’aikacin POS ya kai rahoto ga ‘yan sanda cewa ɗaya daga cikin kwastomominsa da har yanzu ba a gano ba, ya yi kuskuren tura masa naira miliyan 10 maimakon naira dubu 10.

Kiyawa ya bayyana cewa, bayan samun rahoton, Kwamishinan ‘Yan Sandan, Usaini Gumel, ya bayar da umarnin gudanar da bincike na gaskiya da nufin zaƙulo mai kuɗin domin a mayar masa da kuɗin sa.

Ya ce ƙungiyar ‘yan sandan ta ɗauki watanni uku kafin ta gano ainihin mai kuɗin.

“A ranar 14 ga Maris, an kammala bincike a kan gano ainihin mai kuɗin, wanda ya kasance ɗan kasuwa a shahararriyar Kasuwar Hatsin Dawanau da ke Dawakin Tofa.

“Mai kuɗin (an sakaya sunansa) ya yaba wa ma’aikacin POS da ‘yan sanda bisa ƙoƙarin da suka yi kuma saboda murna ya miƙa kyautar kuɗi naira 500,000 ga ma’aikacin POS.

“Ya kuma yaba wa Kwamishinan bisa yadda ‘yan sanda suka nuna gaskiya da riƙon amana, yana mai cewa wannan nuni ne na shugabanci nagari,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?