Ma’aikatan gwamnati a jihar Neja sun bayyana fara yajin aikin sai baba-ta-gani saboda gazawar gwamnati wajen biyan buƙatun su.
Ma’aikatan da ke aiki a ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya reshen jihar, sun gabatar da wasu buƙatu ga gwamnatin jihar waɗanda ƙungiyar NLC ta ce jihar ta kasa cika alƙawarin da ta ɗauka a kansu.
Sai dai ta ce ƙofofinta a buɗe suke domin tattaunawa.
Ƙungiyar a cikin wasiƙar da ta aike wa Gwamna Mohammed Bago mai kwanan wata sha tara ga watan Fabrairu mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, Idrees Lafene, da shugaban Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa, Ibrahim Gana, ta ce za a fara yajin aikin da ƙarfe 8 na safe ranar Laraba ashirin da ɗaya ga Fabrairu, 2024.
An miƙa wa manema labarai wasiƙar a ranar Talata. Wasiƙar ta ce “Muna rubutu ne dangane da wasiƙarmu ta farko ta kashedi na ƙarshe Ref no. OL/NS/040/GEN/Vol 4/29 mai dauƙe da kwanan wata 20/12/23 da kuma tsaikon da aka samu na sasanta al’amura sakamakon tattaunawa da kwamitin gwamnatin jihar Neja.
“Muna so mu sanar da gwamnati a hukumance cewa daga ƙarfe takwas na safe ranar Laraba ashirin da ɗaya ga Fabrairu, 2024, ma’aikatan jihar Neja za su fara yajin aikin sai baba-ta-gani har sai an biya mana buƙatunmu gaba ɗaya.
“A halin yanzu, muna so mu sake nanata cewa ƙofofinmu a buɗe suke don yin shawarwari dangane da: Isar da gayyata ta hukuma, soke duk wasu naɗe-naɗen da ke cikin rigima, watau, Manyan Daraktoci na Kuɗi, Manyan Daraktocin Gudanarwa da Manyan Daraktocin Ayyuka, Ciyaman, Membobi da kwamishinonin dindindin na Hukumar Ayyukan Gwamnati da Hukumar Ma’aikata, Manyan Daraktoci na wasu hukumomi.m
“Bayanin sanarwa daga gwamnati kan biyan albashin ma’aikata.
“Muna kuma so mu jaddada cewa Ƙungiyar Ƙwadago ba za ta ƙara amincewa da naɗa Sakatarorin Dindindin waɗanda ba su cancanta ba a cikin aikin.
“Saboda haka muna kira ga gwamnati da ta janye naɗin wucin gadi na wani mataimakin shugaban makaranta a matsayin Sakatare na dindindin don ba da damar ci gaban aiki daga ciki.
“Muna kuma kira ga gwamnati da ta daina cin zarafin malamai da ‘yan ƙungiya a ɓangaren ilimi sakamakon muhawarar da wasu ɗaliban firamare suka yi a ƙaramar hukumar Agaie.”
Ƙungiyar ƙwadagon ta nanata ƙudurin ta ga ajandar Sabuwar Nijer na gwamnan, tare da lura da cewa babu wani martani ga wasiƙun da aka aika a baya.