Back

Ma’aikatan gwamnatin Jigawa sun ki amincewa da biyan albashin N10,000 daga ragin tallafin man fetur

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC da kuma kungiyar ‘yan kasuwa, TUC a jihar Jigawa sun yi watsi da batun biyan albashin N10,000 da gwamnatin jihar ta gabatar a matsayin wani tallafi daga rage tallafin man fetur.

An bayyana kin amincewa da hakan ne a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan wani taron kungiyar kwadago a jihar da aka gudanar a Dutse babban birnin jihar.

Sanarwar ta hadin guiwa wadda shugabannin kungiyoyin NLC da TUC suka sanya wa hannu, sun bayyana cewar ba a Kai ga matsaya ba game da sanarwar da gwamnatin jihar ta yi na bayar da albashin ma’aikata.

Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa, kwamitin tattaunawa kan albashin na kungiyar’yan kodagon, ya dauki tsawon lokaci yana tattaunawa da kwamitin gwamnatin jihar, inda suka gabatar da bayanai daban-daban ba tare da samun gamsasshiyar amsa ba.

Kungiyar Kwadago ta bayyana mamakin ta ga Kwamishinan Yada Labarai, Matasa da Al’adu na Jihar, Sagiru Musa game da bayyana kyautar N10,000 na albashin watanni uku.

“Yana da kyau jama’a su lura cewa kungiyar kwadagon ba ta sanya hannu kan wata takardar yarjejeniya da gwamnatin jihar Jigawa kan biyan albashin N10,000 ba; Kwamitin Tattaunawar bai kammala aikinsa ba,” in ji ‘yan kodagon.

Sai dai da aka tuntubi shugaban ma’aikata na jihar, Muhammad K. Dagacire domin jin ta bakin sa, ya bayyana cewa kwamitin sulhu na NLC yana da cikakkiyar masaniya kan matakin da gwamnatin jihar ta dauka dangane da matakan kwantar da tarzoma ga ma’aikata.

Dagacire ya bayyana cewa yarjejeniyar ta hada da bayar da kyautar albashi na watanni uku, raba kayan abinci, da samar da kayan amfanin gona gami da filaye ga kowane ma’aikacin gwamnati.

“Don haka abin mamaki ne jin wannan labari daga gare ku kan NLC ta ki amincewa da N10,000.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?