Back

Ma’aikatar Wasanni Ta Haɗa Kai Da Sojoji Don Ci Gaban ‘Yan Wasa

Ministan raya wasanni na Najeriya, Sanata John Enoh, ya yi alkawarin yin aiki tare da sojoji da cibiyoyin soja don bunkasa ’yan wasa kwararru a duniya, wadanda za su iya samun lambobin yabo na kasa da kasa ga kasar.

Sanata Enoh ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a gasar Judo ta sojoji a karo na farko a Abuja.

Ya bayyana takaicin shi ganin yadda cibiyoyin soji da a wasu lokutan baya suka taba samar da ‘yan wasa kwararru masu basirar wasanni, amma a yanzu kuma abin ya lalace har na tsawon shekaru masu yawa, yana mai kira da a farfado da wannan dabi’ar.

Ya kuma kara karfafa gwiwar sauran kungiyoyin wasanni da su bi sawun wadanda suka shirya wannan gasar kuma su kulla kawance da sojojin da cibiyoyin soja, domin inganta damar da kasar za ta samu wajen halartar gasar.

Sanata Enoh ya yi alkawarin ci gaba da bayar da goyon baya ga bunkasar wasanni daban-daban a kasar nan, kuma yace idan a karkashin shugabancin shi Judo ya koma matakin da ya dace na farko a cikin wasanni, to, ya samu nasarar aikin shi a matsayin shi na minista.

Ministan ya yabawa kungiyar Judo ta Najeriya da ta fara gasar Judo ta soja a ƙasar.

Shugaban kungiyar Judo ta Najeriya Musa Oshodi, ya jaddada cewa manufar hadin gwiwa tsakanin hukumar da sojoji shi ne tabbatar da cewa Judo ya dawo da martabar shi a Najeriya.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?