Back

Mafi ƙarancin albashi: NLC ta buƙaci N794,000; TUC, N497,000

A jiya ne Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya, NLC, ta gabatar da Naira 794,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikatan Nijeriya yayin da Ƙungiyar Ƙwadago ta TUC ta ba da shawarar Naira 497,000 yayin zaman sauraron ra’ayin jama’a na shiyyar Kudu maso Yamma kan mafi ƙarancin albashin ma’aikata da aka gudanar a Legas.

Zaman, wanda kwamitin uku da ke kula da mafi ƙarancin albashi na ƙasa ya shirya, na ɗaya daga cikin shidan da aka gudanar a lokaci guda a shiyyoyin ƙasar nan shida.

Shugabar Ƙungiyar NLC reshen jihar Legas, Kwamared Funmi Sessi, wacce ta bayar da shawarar Naira 794,000, ta ce ya kamata a ci gaba da biyan mafi ƙarancin albashin ma’aikata na ƙasa a cikin keɓantaccen jeri, sannan a dinga bitar sa duk bayan shekaru biyu maimakon shekaru biyar.

Tun da farko, a jawabinsa na maraba, Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki, Mista Yemi Edun ya ce kwamitin na da sha’awar samar da takardun matsayi mai kyau da za su taimaka wajen yanke shawarar da ta dace.

A wani labarin kuma, an gudanar da taron jin ra’ayin jama’a na shiyyar Arewa maso Gabas kan kwamitin uku na mafi ƙarancin albashi na ƙasa a Yola a ranar Alhamis, inda ɗaya daga cikin gwamnonin yankin ya gabatar da wata sabuwar hanyar raba kuɗaɗen shiga.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, ya gabatar da shawarar ƙarin mafi ƙarancin albashin ma’aikata, inda ya yi kira da a ƙara Naira 45,000 da za a inganta tare da sake duba tsarin rabon albashin.

Ya ba da shawarar cewa gwamnatin tarayya ta samu kashi 35, jihar ta samu kashi 40, ƙaramar hukumar kuma ta samu kashi 25.

Gombe, Taraba, Adamawa, Yobe da Borno duk sun sami wakilai a zaman, inda jihohin biyu na farko suka ba da shawarar Naira 60,000 sai Adamawa ta ba da shawarar Naira 45,000 ga ma’aikatansu duka.

A halin da ake ciki kuma sassan Kudu maso Gabas na NLC da TUC, sun gabatar da N540,000 da N447,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan Nijeriya.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya, NAN, ya ruwaito cewa ƙungiyoyin ƙwadago ta NLC da TUC ne suka gabatar da wannan ƙudiri yayin zaman na shiyyar Kudu maso Gabas a Enugu.

Shugaban Ƙungiyar NLC reshen jihar Enugu, Kwamared Fabian Nwigbo, ya bayyana cewa tsadar farashin kayayyaki ta ragu da darajar mafi ƙarancin albashi na Naira 30,000 na shekarar 2019.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?