Back

Mahara sun kashe kwamandan sojoji, Manjo 2, Kyaftin 1, da wasu a Delta

A ranar Asabar ne Rundunar Ƙoli ta Sojoji ta sha alwashin bin diddigin wasu matasa, waɗanda rahotanni suka ce sun kashe jami’anta 16 da ke aiki da Bataliyar 181 Amphibious a ƙaramar hukumar Bomadi ta jihar Delta.

An ruwaito cewa an samu matsala ne a ranar Alhamis lokacin da sojojin suka amsa kiran da suka yi na neman ɗauki game da rikicin ƙabilanci tsakanin al’ummar Okuoma da Okoloba.

Daraktan Yaɗa Labarai na Soji, Tukur Gusau, wasu matasan al’umman da ke ɗauke da makamai suka kewaye sojojin sannan suka kashe su.

Babban jami’in sojan ya ce ‘yan bindigar sun kashe kwamandan, Manjo biyu, Kyaftin ɗaya, da sojoji 12. Ya ƙara da cewa an kai rahoto ga gwamnatin jihar Delta.

A cewarsa, Shugaban Hafsan Sojin Ƙasa, Janar Christopher Musa, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da damƙe waɗanda ke da hannu a wannan ɗanyen aikin.

Ya ce, “Dakarun Bataliyar 181 Amphibious, ƙaramar hukumar Bomadi ta jihar Delta a yayin da suke aikin samar da zaman lafiya a yankin Okuoma, wasu matasan al’umma sun kewaye su tare da kashe su a ranar Alhamis, 14 ga Maris, 2024.

“Abin takaicin ya faru ne lokacin da sojojin suka amsa kiran gaggawa bayan rikicin ƙabilanci tsakanin al’ummar Okuoma da Okoloba duk a jihar Delta.

“An kuma kai wa tawagar dakarun da ke ƙarƙashin jagorancin kwamandan hari, wanda ya yi sanadin mutuwar kwamandan, Manjo biyu, Kyaftin ɗaya da sojoji 12.

“Shugaban Hafsan Sojin Ƙasa, Janar Christopher Gwabin Musa, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da cafke waɗanda ke da hannu a wannan ɗanyen aikin. Tuni dai aka kai rahoton faruwar lamarin ga gwamnatin jihar Delta.

“Duk da haka, sojojin sun ci gaba da mai da hankali da kuma jajircewarsu wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ƙasar nan. Ya zuwa yanzu, an kama wasu yayin da ake ɗaukar matakai domin bankaɗo maƙasudin kai harin.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?