Majalisar Dattawa ta dawo da Sanata Abdul Ahmed Ningi, wanda ke wakiltar Bauchi ta tsakiya, bayan dakatar da shi a ranar 12 ga Maris, 2024.
An dakatar da Ningi ne saboda zargin da ya yi wa Majalisar Dattijai na ƙara kasafin kuɗi.
An dawo da shi makonni biyu kafin ƙarshen dakatarwar da aka yi masa na tsawon watanni uku wanda ya kamata ya kare a ranar 12 ga Yuni, 2024.
A ranar Talata ne dai aka fara shirin dawo dashi bayan wani ƙudiri da Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye, Sanata Abba Moro ya gabatar, wanda ya nuna nadamarsa a madadin Sanatan da aka dakatar.
Moro ya yi alƙawarin ɗaukar cikakken alhakin abinda Ningi ya aikata, tare da amincewa da girman dakatarwar.
Shugaban Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio, ya bayyana kiran da aka yi wa Ningi ba tare da wani sharaɗi ba, bayan wasu ‘yan majalisar sun yi wata ‘yar gajeruwar roƙo.