Majalisar Dattawa a ranar Alhamis 9 ga watan Mayu ta amince da hukuncin kisa ga waɗanda aka samu da laifin safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasar.
Hukuncin da aka tanada a cikin dokar Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Muggan Ƙwayoyi ta Kasa (NDLEA) shine mafi girman hukunci na ɗaurin rai da rai.
Kuɗurin Majalisar ya biyo bayan nazarin rahoton Kwamitocin Harkokin Shari’a, ‘Yancin Ɗan Adam da Al’amuran Shari’a da Magunguna da Miyagun Ƙwayoyi, Dokar Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Muggan Ƙwayoyi ta Kasa (NDLEA) (gyara) ta shekarar 2024.
Shugaban Kwamitin Kula da Harkokin Shari’a, ‘Yancin Ɗan Adam da Al’amuran Shari’a, Sanata Mohammed Monguno (APC-Borno North), ne ya gabatar da rahoton a zaman majalisar.
Ƙudirin dokar, wanda ya tsallake karatu na uku, yana da nufin sabunta jerin magunguna masu haɗari, da ƙarfafa ayyukan hukumar NDLEA, da sake duba hukunce-hukunce, da kuma ba da damar kafa ɗakunan gwaje-gwaje.