Back

Majalisar Dattawa ta amince da kafa Hukumar Raya Arewa Maso Yamma

A ranar Alhamis ne Majalisar Dattijai ta amince da ƙudirin dokar kafa Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma (NWDC) domin magance matsalolin da jihohi bakwai na shiyyar ke fuskanta.

Wannan ya biyo bayan la’akari da amincewa da rahoton Kwamitin Ayyuka na Musamman akan kafa NWDC.

Ƙudirin dokar wanda ya wuce karatu na uku ya samu ɗaukar nauyin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, da wasu ‘yan majalisa 20 daga jihohi bakwai na shiyyar Arewa maso Yamma.

Shugaban Kwamitin, Sanata Shehu Kaka (mai wakiltar Borno ta tsakiya) wanda ya gabatar da ƙudirin gabatarwa da la’akari da rahoton, ya ce an tsara ƙudirin da kuma maƙasudin ƙudurin don bunƙasa zamantakewa da tattalin arziƙin shiyyar Arewa maso Yamma na ƙasar.

Ya kuma ƙara da cewa kafa hukumar zai ƙara kusantar Gwamnatin Tarayya da jihohin Arewa maso Yamma da kuma biyan buƙatun jama’a.

Bayan kafa Hukumar Raya Neja-Delta (NDDC) da Hukumar Cigaban Arewa maso Gabas (NEDC), wasu shiyyoyin sun fara neman kwamitocinsu.

An kafa hukumar NEDC ne biyo bayan ɓarnar da mayaƙan Boko Haram suka yi a yankin Arewa maso Gabas.

Ana kuma shirin kafa Hukumar Raya Yankin Kudu maso Gabas.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?