Back

Majalisar Dattawa Ta Bukaci Daliban Da Suka Kammala Karatun Likitanci A ƙasar Ukraine, Sudan Su Zauna Jarrabawar Cancanta 

Majalisar dattawa ta Najeriya ta bukaci hukumar kula da lafiya da hakora ta ƙasar (MDCN) da ta kyale ‘yan Najeriya da suka kammala karatun likitanci a kasashen Ukraine da Sudan, wuraren da yaki bai shafi karatun su ba da Ɗaliban su zauna jarrabawar ta a watan bakwai da watan sha daya ba tare da nuna banbanci ba.

Haka kuma ta bukaci hukumar da ta himmatu wajen gudanar da jarrabawar ta a kowanne shiyyar siyasa ta kasar nan kamar Makarantun Shari’a, domin rage tsadar kudin da dalibai da iyayen su ke kashewa.

Kudirin majalisar dattawan ya biyo bayan amincewa da wani kudiri ne a zauren majalisar a ranar Talata.

Kudirin mai taken: “Wariya ga daliban da suka kammala karatun likitanci daga kasar Ukraine da Majalisar Likitoci da Hakora ta Najeriya ta dauki nauyi Sanata Oyewumi Olalere (PDP- Osun).

Olalere a muhawarar da ya jagoranta ya ce batun daliban da suka kammala karatun likitanci a jami’o’in Ukraine ya ja hankalin majalisar dokokin kasar tun daga shekarar ta dubu biyu da ashirin da biyu.

Ya ce a cikin shekara ta dubu biyu da ashirin da uku, Majalisar Wakilai da Ma’aikatar lafiya tare da Majalisar Likitocin hakora sun aminta kan baiwa  daliban da suka kammala karatun likitanci a ƙasar Ukraine damar su shiga jerin wadanda za su zauna jarrabawar  cancantar kamar sauran ɗalibai.

Ya ce hukumar ta tsara shirin jarrabawar wadanda suka kammala karatu a shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu kadai ne a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Gwagwalada akan kudi Naira miliyan daya da rabi kan kowanne dalibi da za a biya a cikin mako daya da rabi.

Sauran Sanatocin da suka goyi bayan kudirin sun hada da Sanata Adamu Alero (PDP- Kebbi), Abdul Ningi (PDP-Bauchi) da dai sauran su.

Majalisar dattawan ta kuma bukaci kwamitin mataimakan shugabannin Najeriya da su kyale daliban Najeriya da ke shigowa daga kasashen da yaki ya farraka su da su shiga jami’o’in Najeriya domin kammala karatun su.

A nasa jawabin shugaban majalisar dattawa Godswill Akpiabio, ya godewa wanda ya dauki nauyin wannan kudiri, inda ya ce wannan kudiri ne na jama’a da kuma tsokaci daga ‘yan majalisar.

Ya bayyana imanin cewa MDCN da mataimakan shugabanni jami’o’i za su bi kudurorin majalisar dattawan domin magance matsalolin da ke addabar dalibai ‘yan Najeriya da suka kammala karatun likitancin daga kasashen da yaki yayi masu illa.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?