Majalisar dattijai ta dage sauraren karar da ake yi wa hafsoshin tsaron Najeriya kan rashin samar da tsaro zuwa ranar 13 ga watan Fabrairu na wannan shekarar domin sauraron duk wani mai hannu a da tsaki a harkokin tsaro na kasar.
A ranar larabar da ta gabata ne shugabannin tsaron suka halarci zauren majalisar dattijan domin yiwa ‘yan majalisar jawabi kan matsalar rashin tsaro a kasar Najeriya, daga baya aka sauya shawarar dage taron zuwa wani lokaci.
Shugaba a majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele ne ya gabatar da kudirin dage zaman taron tsaron da shugabannin hukumomin tsaro suka gabatar kuma shugaban marasa rinjaye na majalisar, Sanata Abba Moro ya amince da shi.
Shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio yayin da yake amincewa da dage zaman, ya bayyana cewa majalisar za ta so yin cikakken nazari kan rashin tsaro.
Daga bisani an umurci magatakardar majalisar dattijan da ya fadada jerin sunayen wadanda aka gayyata da suka hada da dukkan Shugabannin Ma’aikata, Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, ministan kudi, ministan cikin gida, ministan tsaro, karamin ministan tsaro da ministan harkokin ‘yan sanda.
Majalisar dattijan ta yanke hukuncin bai daya bayan wani zaman gaggawa da ta yi a ranar farko na majalisar a ranar 30 ga watan Janairu inda ta gayyaci hafsoshin tsaron kasar saboda tabarbarewar tsaro a Najeriya.
Hafsan hafsoshin da suka halarci taron a yau sun hada da babban hafsan tsaron kasa (CDS), Janar Christopher Musa; Babban Hafsan Sojoji (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja; Babban Hafsan Sojan Sama (CAS), Air Marshal Hassan Abubakar, da Shugaban Rundunar Sojojin Ruwa (CNS), Vice Admiral Emmanuel Ogalla.