Back

Majalisar Dattawa ta dakatar da Ningi na watanni 3

Sanata Abdul Ningi

Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon watanni uku saboda cece-ku-ce kan kasafin kuɗin 2023.

An dakatar da Ningi ne biyo bayan zargin da ya yi na ƙarin kasafin kuɗi naira tiriliyan 3.7 a wata hira da BBC Hausa.

Ningi a ranar Litinin ya musanta iƙirarin da ya yi a cikin hirar, yana mai cewa ba a fahimce shi ba.

Kafin dakatar da Ningi, ‘yan Majalisar Dattawa da suka fusata sun yi muhawara kan zargin wanda ya jefa majalisar cikin wani zama mai cike da ruɗani.

Da yake magana a matsayin baƙo a wata hira da BBC a ranar Asabar, Sanatan ya bayyana cewa jiga-jigan Arewa basa farin ciki da wannan gwamnati saboda an yi watsi da Arewa.

Ya ce, “Wannan gaskiya ne (game da batun bitar gwamnati) tsawon watanni uku da suka gabata, mun ɗauki masu ba da shawara da za su duba mana kasafin kuɗin. Muna da wasu ƙwararrun da ke aiki akan sa layi-layi. Mun ga irin ɓarnar da aka yi ba ga arewa kaɗai ba har ma da ƙasa baki ɗaya a kasafin kuɗin. Ya kamata mu zauna da Shugaban Majalisar Dattawa don sanar da shi abin da muka lura.”

Amma bayan zaman da aka yi a Majalisar Dattawa, an dakatar da Sanatan mai wakiltar Bauchi ta tsakiya.

Cikakkun bayanai daga baya…

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?