Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce nan ba da daɗewa ba Majalisar za ta ɗage dakatarwar da ta yi wa Sanata Abdul Ningi (PDP, Bauchi ta Tsakiya).
Hakan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da ɗan majalisar ya rubuta wa Akpabio wasiƙa, inda ya yi barazanar ɗaukar matakin shari’a idan ba a ɗage dakatarwar da aka yi masa ba cikin kwanaki 7 ba.
An dakatar da Ningi ne biyo bayan hirar da ya yi da BBC Hausa inda ya yi zargin cewa an yi ƙari a kasafin kuɗin shekarar 2024 da naira tiriliyan 3.7.
Bayan zazzafar muhawara da Sanatoci suka yi a zauren majalisa kan lamarin, an dakatar da Ningi na tsawon watanni uku tare da neman ya rubuta wasiƙar neman gafara ga majalisar.
Sai dai a wata takarda da lauyan sa Femi Falana (SAN) ya rubuta, Ningi ya zargi Akpabio da kasancewa mai tuhuma, mai gabatar da ƙara da kuma alƙali a shari’ar da ya ce ya saɓawa tanadin kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999.
A cikin wasiƙa mai taken; ‘Buƙatar a ɗage dakatarwar da aka yi wa Sanata Abdul Ahmed Ningi,’ mai kwanan wata Laraba, 27 ga Maris, 2024, Sanata Ningi ya yi barazanar zuwa kotu.
Sanatan ya zargi Akpabio da sa aka gurfanar da shi a gaban Majalisar Dattawa a ranar 14 ga Maris, 2024 wanda ya saɓa wa tanade-tanaden dokar Majalisar Dokoki (Iko da Gata), 2018.
Sai dai da yake amsa tambayoyin manema labarai a ranar Juma’a da ya isa taron ƙungiyar ‘yan Majalisar Dokokin Ƙasar a birnin Geneva na ƙasar Switzerland, Akpabio ya ce nan ba da daɗewa ba Majalisar Dattawa za ta duba dakatarwar na tsawon watanni uku.
Ya ce, “Wannan hukunci ne na Majalisa. Har yanzu ban ga wasiƙar ba. Amma Sanata Ningi yana ɗaya daga cikin mu. Ina nufin menene dakatarwa? Na yi imani cewa nan da ‘yan kwanaki, zai kasance tare da mu. Don haka, babu matsala. Za a warware shi cikin ruwan sanyi. Majalisar Dattawa iyali ce.”
An ruwaito cewa dakatarwar Ningi ba zai wuce watanni uku ba. Wani babban ɗan Majalisar Dokokin ya shaida cewa ana nan ana warware matsalar cikin ruwan sanyi.
An dai sha matsin lamba ga Majalisar Dattawa ta sake duba matakin da ta ɗauka wanda ake ganin bai dace ba a wasu ɓangarori.