Majalisar Dokokin Jihar Kano ta soke dokar da ta kafa sabbin masarautu guda 5 a jihar.
An rushe duk ofisoshin da aka kafa a ƙarƙashin dokar da aka soke da sabon ƙudirin.
Haka kuma duk masu unguwa da aka ɗaukaka ko aka naɗa a ƙarƙashin dokar da aka soke za su koma kan muƙamansu na baya.
Shugaban masu rinjaye kuma memba mai wakiltar mazaɓar Dala, Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa ne ya ɗauki nauyin Dokar da ta kafa Masarautun Jihar Kano (gyara mai lamba 2) ta 2024.
Tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya fara sanya hannu a kan Dokar wadda ta kafa sabbin masarautu guda biyar a ranar 5 ga Disamba, 2019.
Gwamnan ya amince da gyara dokar a ranar 14 ga Oktoba, 2020 tare da sanya hannu kan wani gyara a ranar 11 ga Afrilu, 2023.