Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ƙudiri aniyar yiwa Dokar Sarakunan Kano kwaskwarima a daidai lokacin da ake kira da a dawo da tsohon Sarkin Kano na 14, Muhammad Sanusi.
Majalisar ta yanke shawarar gyara dokar ne bayan shugaban masu rinjaye kuma memba mai wakiltar mazaɓar Dala, Hussien Dala, ya gabatar da ƙudirin yayin zaman majalisar a ranar Talata.
Daily Trust ta ruwaito cewa an fara gyara dokar ne a shekarar 2019 a lokacin da ake takun saƙa tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Sarkin.
Canjin na farko dai ya raba masarautar Kano zuwa masarautu biyar daban-daban inda aka ƙirƙiro masarautu na Rano, Karaye, Gaya da Bichi, sannan aka naɗa sarakuna a sabbin masarautun, wanda a ƙarshe ya kai ga tsige Sarkin Kano na wancan lokacin.
Amma bayan nasarar zaɓen Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya yi amfani da maido da tsarin masarautar Kano wajen yaƙin neman zaɓe, ƙungiyoyi da dama sun sabunta kiran a dawo da Sarki Sanusi.