Back

Majalisar Jahar Zamfara ta dakatar da ‘ya’yan ta guda takwas

Shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara, Bilyaminu Moriki da wasu ‘yan majalisar guda shida a zaman da suka yi a ranar Litinin sun dakatar da ‘yan majalisar guda takwas da suka yi barazanar tsige shugaban majalisar a ranar Alhamis din da ta gabata.

Da yake gabatar da kudirin dakatar da ‘yan majalisar, shugaban masu rinjaye Muhammad Mazawaje, ya ce ana zargin ‘yan majalisar ne da kutsa kai cikin ofishin magatakardar majalisar da kuma lalata wasu abubuwa a harabar majalisar.

Mambobi takwas da majalisar ta dakatar sun hada da, Hon Sani Abdullahi, Hon Nasiru Mar, Hon Bashir Abubakar, Hon. Aminu Keta, Hon. Faruk Musa Dosara, Hon. Bashir Aliyu, Hon. Ibrahim T. Tukur da Hon. Shamsuddeen Hassan.

Shugaban majalisar ya bayyana zaman ‘yan majalisar takwas da suka yi a ranar Alhamis din da ta gabata a matsayin wanda ya sabawa doka, yana mai jaddada cewa matakin da suka yi na rusa wasu ofisoshin majalisar domin gudanar da zaman ba bisa ka’ida ba ya saba wa ka’idojin majalisa.

A kan kudirin dakatarwar da shugaban masu rinjaye ya gabatar, Muhammad Mazawaje ya ce “’yan majalisar da aka dakatar sun shirya yi zama ba bisa ka’ida ba, ba tare da mataimakin shugaban majalisar ba a ko shugaban majalsar, tare da rufe babbar kofar shiga harabar majalisar da nufin hana sauran mambobin majalisar shiga.”

A nasu gudunmuwar da suka bayar a lokacin da suke goyon bayan kudurin dakatarwar, mataimakin kakakin majalisar, Lirwanu Marafa Anka da Hon Hamisu Faru, dukkan su sun bayyana abin da ya faru a majalisar dokokin jihar a matsayin wanda ya sabawa majalisar, inda suka ce bai kamata a dauki matakin da wasa ba, suna goyon bayan kowa.

 ‘Yan majalisar sun kuma yi zargin cewa sun rufe kofar majalisar ne a wani shiri na hana sauran mambobin majalisar shiga harabar majalisar.

Mambobin takwas tare da wasu a karkashin jagorancin kakakin majalisar a ranar Alhamis din da ta gabata a zaman su sun dakatar da kakakin majalisar Bilyaminu Moriki tare da rufe majalisar har sai mama ta gani.

‘Yan majalisar su shida a jawaban su daban-daban a zaman na yau Litinin sun zargi wasu jiga-jigan ‘yan siyasa da ke wajen jihar da daukar nauyin ‘yan majalisar goma sha takwas domin kawo cikas ga kyakkyawar kimar majalisar da kuma na gwamnatin Gwamna Dauda Lawal.

Sun kuma yi kira ga ‘yan majalisar da abin ya shafa da jama’ar jihar da su yi watsi da abin da wasu ‘yan majalisar su goma sha bakwai suka yi na cewa an dakatar da shugaban majalisar.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?