Back

Majalisar Wakilai ta ƙara albashin CJN zuwa naira miliyan 5.3 a duk wata, alƙalan Kotun Ƙoli naira miliyan 4.2

A ranar Laraba ne Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar neman ƙarin albashi da alawus-alawus ga masu riƙe da muƙaman shari’a a ƙasar.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa Majalisar ƙudirin dokar domin tantancewa tare da amincewa da shi a ranar Talata.

Ƙudirin da aka amince da shi ya bayar da jimillar naira 5,385,047.26 a kowane wata ga Babban Alƙalin Nijeriya (CJN).

Ƙudirin ya ce sauran alƙalan Kotun Ƙoli za su samu jimillar naira 4,213,192.54, yayin da Shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙara zai riƙa samun jimillar naira 4,478,415.78 duk wata.

Har ila yau, alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙara za su riƙa karɓar jimillar kuɗi naira 3,726,665.40 duk wata, yayin da Babban Alƙalin Babbar Kotun Tarayya, Shugaban Kotun Masana’antu ta Ƙasa, Babban Alƙalin Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya, Babban Khadi na Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Sharia, da Shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙara na Jiha, zasu samu jimillar naira 3,527,022.61 duk wata.

A cewar ƙudirin, albashin na wata-wata ya ƙunshi cikakken albashin su da duk wani alawus-alawus na yau da kullum da suka haɗa da samar da mai da kuma lura da mota da dai sauransu.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?