Back

Majalisar Wakilai ta amince da muhawara a kan ƙudurin dokar kafa ‘yan sandan jihohi

Majalisar wakilai a ranar Talata, ta amince da muhawara a kan ƙudirin dokar kafa ‘yan sandan jihohi a ƙasar.

Ƙudirin wanda Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu da wasu mutane sha huɗu suka ɗauki nauyi, na neman sauya sassan da suka dace na kundin tsarin mulkin ƙasar na 1999 domin share wa jihohi fagen kafa nasu ‘yan sandan.

Yayin da ‘yan majalisar ke bi – da bi wajen bayar da tasu gudunmawar a zauren majalisar a zaman majalisar na yau ranar Talata, Kalu wanda ya tsaya wa shugaban majalisar, Abbas Tajudeen, ya buƙaci ‘yan majalisar da kada su yi la’akari da burin su na siyasa, su yi tunanin kare lafiyar ‘yan Najeriya da Najeriya.

Shi ma da yake magana, Babajimi Benson (APC, Legas) ya ce, “Aikin ‘yan sanda ne su tabbatar da doka da oda. Muna da yawan jama’a sama da miliyan ɗari biyu amma muna da ƙarfin ‘yan sanda wanda bai wuce dubu ɗari huɗu ba. Yakamata a samar da ‘yan sandan jahohi domin magance matsalolin tsaron cikin gida na Najeriya.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?