Majalisar Wakilai ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta hannun Ma’aikatarta ta Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari da ta gaggauta dakatar da sanya hannu da kuma aiwatar da hulɗar kasuwanci da ƙasar Burtaniya.
Majalisar ta ce ya kamata a dakatar da yarjejeniyar har sai an yi nazari sosai tare da tantancewa da fahimtar sharuɗɗan da suka gindaya mata.
Ƙudurin ya biyo bayan ƙudirin da ɗan Majalisar Wakilai Kingsley Chinda (PDP-Rivers) ya gabatar a zauren majalisa a Abuja ranar Talata.
Da yake gabatar da ƙudirin, Chinda ya bayyana cewa, haɗin gwiwar tattalin arziƙi da kasuwanci tsakanin Burtaniya da Nijeriya na da nufin gano sabbin damammaki a muhimman sassa kamar makamashi, shari’a, da harkokin kuɗi.
Ya ce yarjejeniyar cinikin ta ƙara ƙarfi yayin da ɓangaren shari’a ya bayyana ya karkata musamman ga amfanin ƙasar Burtaniya don cutar da ƙwararrun lauyoyin Nijeriya.
Ya ƙara da cewa yarjejeniyar ta nemi a baiwa lauyoyin Burtaniya damar shiga fagen shari’ar Nijeriya su yi aiki amma akasin haka ga lauyoyin Nijeriya.
A cewarsa, yayin da yarjejeniyar ke neman samar da haɗin gwiwa tsakanin masana’antun fina-finai da na yaɗa labarai a Burtaniya da Nijeriya, ba ta cimma muradun lauyoyin Nijeriya ba.
Ya ƙara da cewa babu irin wannan tanadi ko damar da za su iya gudanar da aikin su a Burtaniya.
Ya ce duk da cewa yana da kyau Nijeriya ta ƙulla hulɗar haɗin gwiwa da wasu ƙasashe, dole ne irin waɗannan yarjejeniyoyin su inganta, su kiyaye, kuma su kare muradun ‘yan Nijeriya gaba ɗaya.
Ya ce akwai buƙatar majalisar ta gaggauta binciken yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Burtaniya da Nijeriya domin fahimtar sharuɗɗan.
“Sai dai idan ba a ɗauki matakin gaggawa don bincikar lamarin ba, Nijeriya na iya shiga cikin hulɗar da sharuɗɗan ba za su yi wa ƙasar daɗi ba.”
Da take amincewa da ƙudirin, majalisar ta umurci kwamitinta mai kula da yarjejeniyoyi da ƙa’idoji da ya binciki lamarin tare da bayar da rahoto cikin makonni huɗu domin ci gaba da aiwatar da dokar.