Majalisar Wakilai a ranar Laraba ta umarci kwamitocinta masu kula da harkokin bankuna da su binciki yadda Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sallami ma’aikata kusan 600 ba bisa ƙa’ida ba.
Matakin ya biyo bayan amincewa da ƙudirin da ɗan majalisar wakilai Jonathan Gaza Gbefwi (Nasarawa, SDP) ya gabatar.
Gbefwi, a cikin ƙudirin nasa, ya ce CBN a wani ɓangare na gyare-gyaren da ta ke yi, na rage ma’aikata, cikin su har da daraktoci.
Ɗan Majalisar ya ce sallamar ma’aikatan ba bisa ƙa’ida ba zai daƙushe ƙwarin gwiwa da ƙwazon ma’aikata.
Ya kuma ce ƙasar nan ba za ta iya watsar da ma’aikatan da aka horar da su waɗanda suka iya aiki ba ta hanyar korar da bankin ƙoli ya yi ba bisa ƙa’ida ba.
An dai amince da ƙudurin gaba ɗaya ne bayan kaɗa ƙuri’a tare da miƙawa kwamitocin kula da harkokin bankuna da su yi bincike tare da bayar da rahoto cikin makonni huɗu.